Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Saturday, June 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKwalejin jinya da unguwar zoma ta Kano na fama da karancin ma'aikata...

Kwalejin jinya da unguwar zoma ta Kano na fama da karancin ma’aikata da matsalar tsaro cewar shugabar makarantar

Date:

Shugabar kwalejin aikin jinya da unguwar zoma ta jihar Kano Mairo Sa’id Muhammad ta ce makarantar na fama da karancin ma’aikata da jami’an tsaro wanda hakan ke barazana ga tsaron makarantar.

Mairo Sa’id ta bayyana hakane yayin da kwamitin harkokin lafiya na majalisar dokokin Kano yakaiwa makarantar ziyara.

Ta ce a kwanakin baya saboda yankewa makarantar wutar lantarki da akayi saida suka fuskanci barazanar masu kwacen waya da suka haura makarantar tare da kwacewa dalibai wayoyi.

Ta kara da cewa a bangaren karatu kwalejin ta samu cigaba ta yadda a yanzu zasu fara bada shedar karatu ta babbar diploma wato HND.

A ziyarar da kwamitin yakai hukumar kula da asusun lafiya ta jihar Kano shugabar hukumar Dakta Fatima Usman Zaharadeen ta ce hukumar na fama da rashin mota da zasu rinka bibiyar ayyukan da hukumar keyi.

Da yake jawabi shugaban
kwamitin lafiya dan majalisa mai wakiltar Kura da Garin Malam Zakariya Alhassan ya ce zasu yi kira ga mai girma gwamnan don ganin an magance matsalolin da suke fuskanta.

Wakilin mu Aminu Abdullahi Ibrahim ya ruwaito cewa Zakariya Alhassan yace majalisa zata tabbatar da cewa n samu lafiya ingattaciya a jihar Kano.

Latest stories

Related stories