Saurari premier Radio
24.9 C
Kano
Wednesday, May 8, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiSaudiya ta kira Najeriya da ministocin kungiyar kasashe musulmi ta OIC kan...

Saudiya ta kira Najeriya da ministocin kungiyar kasashe musulmi ta OIC kan rikicin Isira’ila da Falatsinawa.

Date:

Saudia ta kira Najeriya da ministocin kungiyar kasashe musulmi ta OIC kan rikicin Isira’ila da Falatsinawa.

Kasar Saudia ta kira taron gaggawa na ministocin kungiyar kasashen musulmi ta OIC don tattaunawa kan rikicin Gaza.

Rahotanni sunce yariman kasar Muhammad Bin Salman ne ya kira taron gaggawar a ranar Talata.

Mambobin kungiyar ta OIC sun fito daga nahiyoyi da suka hada da Saudiya da Iran da Turkiya da Indunusiya da Pakistan.

Inda a nahiyar afurka kuma akwai Najeriya da Senegal da Albaniya da sauran kasashe.

Kungiyar OIC tayi Allah wadarai da amfani da karfin soji da Isira’ila keyi akan Gaza inda ta tuhumi Isira’ila da rashin mutunta yarjejeniyar da kasashen duniya suka cimma.

Rikicin Sudan: Yadda aka bar daliban Najeriya a tsakiyar Sahara

Yarima mai jirangado Muhammad Bin Salman ya kuma sake jaddada goyan bayan Saudiya ga al’ummar Falastsinawa .

Idan za a iya tunawa a ranar shida ga watan da muke ciki ne yaki ya sake barkewa tsakanin Isira’ila da kungiyar Hamas dake Gaza.

Latest stories

Related stories