Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Saturday, May 18, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiRikicin Sudan: Yadda aka bar daliban Najeriya a tsakiyar Sahara

Rikicin Sudan: Yadda aka bar daliban Najeriya a tsakiyar Sahara

Date:

Tafiyar ɗaliban kasar na daga Sudan zuwa Masar ta gamu da tirjiyar kamfanin dake aikin jigilar a tsakiyar Sahara.

Wannan na zuwa ne yayin da direbobin manyan motoci safa-safa dake aikin kwashe daliban suka buƙaci cikon kuɗaɗensu kafin su ci gaba da tafiyar.

Lamarin ya faru ne dai-dai lokacin da direbobin motoci guda bakwai da suka ɗauke su daga birnin Khartoum, suka buƙaci cikon kuɗaɗensu, kafin su ci gaba da tafiya.

Wasu dalibai da aka bari a tsakiyar Sahara sun shaidawa Premier Radio cewa suna cikin mawuyacin hali na rashin abinci da ruwan sha, ga tsananin rana da ake fama da ita.

Jamil Isma’il na daga cikin daliban da yanzu haka suke birnin Khartoom, ya koka kan yadda hukumomin Najeriya suka kasa kwashe su zuwa kasar Masar.

Ya ce har kawo yanzu basu san makomar su a, yayin da aka basu wa’adi kan su tashi daga inda suke.

 

Latest stories

Related stories