Saurari premier Radio
31.9 C
Kano
Tuesday, May 21, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiMuna goyon bayan Barau ya zama shugaban majalisar dattawa- Sanata Lado

Muna goyon bayan Barau ya zama shugaban majalisar dattawa- Sanata Lado

Date:

Tsohon sanatan Kano ta tsakiya Sanata Bashir Garba Lado ya ce Sanatan Kano ta Arewa Barau Jibril shi ya fi kowa cancanta ya zama shugaban majalisar dattawa ta goma duba da irin gudunmawar da ya bawa jam’iyyar APC a zaben shekarar 2023 da aka kamala.

Sanata Lado ya bayyana hakan hakan lokacin da ya karbi bakuncin kungiyar matasan arewa dake rajin ganin Sanata Barau ya zama shugaban majalisar dattawa, karkashin jagorancin Musa Mujahid Zaitawa.

Sanata Bashir Garba Lado ya ce a yanzu haka jihar Kano da Arewacin Najeriya basu da Sanata kamar Barau, don haka ya zama wajibi a fito a mara masa baya, domin tabbatar da zaman sa shugaban majalisar dattawa ta goma.

Ya kara da cewa idan Sanata Barau ya samu nasarar zama shugaban majalisar dattawa zai taimaka wajen raya jam’iyyar APC a jiyar Kano tare da kawo ayyukan ci gaba ga jihar.

Tun da fari shugaban kungiyar matasan arewa Musa Mujahid Zaitawa ya bayyana cewa sun kai ziyarar ne domin neman goyon bayan Sanata Lado kan takarar shugabancin majalisar dattawa da Sanata Barau key i.

Mujahid Zaitawa ya ce za su ci gaba da kaiwa masu ruwa da tsaki ziyara domin neman goyon bayan su kan wannan kan wannan yunkuri na ganin sanata Barau ya samu nasara.

Latest stories

Gwamnan Katsina ya nemi tallafi kan karancin abinci da matsalar tsaro ta haddasa.

A wani alk’amarin kuma, Gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda,...

Related stories

Gwamnan Katsina ya nemi tallafi kan karancin abinci da matsalar tsaro ta haddasa.

A wani alk’amarin kuma, Gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda,...