Saurari premier Radio
35.9 C
Kano
Tuesday, May 7, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiBayan biyan kudin fansa masu garkuwa da mutane sun saki daliban jami'ar...

Bayan biyan kudin fansa masu garkuwa da mutane sun saki daliban jami’ar Nasarawa.

Date:

Bayan biyan kudin fansa masu garkuwa da mutane sun saki daliban jami’ar Nasarawa.

Daliban jami’ar jihar Nasarawa hudu da akayi garkuwa dasu a daren ranar Litinin sun shaki iskar ‘yanci bayan biyan kudin fansar da ba a bayyana adadin su ba.

Daliban da suka hada da Rahila da Josephine Gershon da Rosemary Samuel da Goodness Samuel an sace su ne a gidajen kwanan su dake wajen makaranta da karfe 10:30pm.

Rashin kammala kwangilar gyaran ajujuwa a makarantun Kano ya tagayyara karatun dubban dalibai

Rahotanni sunce bayan sakin daliban yanzu haka suna bataliyar soji ta 177 dake birnin Keffi.

Cikin sanarwar da sakataren kungiyar matasa ta jihar Nasarawa Muhammad Sakilu Muhammad ya rabawa manema labarai ta tabbatar da sakin daliban bayan biyan kudin fansa.

Saidai da take tabbatar da sakin daliban rundunar ‘yan sandan Nasarawa ta bayyanawa manema labarai cewa hadin gwiwar jami’an tsaro da rundunar soji ne suka kubutar da daliban.

A baya dai rahotanni sun ce masu garkuwa da mutanen sun nemi kudin fansa naira miliyan 80 domin sakin daliban hudu.

Latest stories

Related stories