Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Tuesday, May 7, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin Lagos ta rufe kasuwar Hausawa ta Mile 12 da Owode Onirin...

Gwamnatin Lagos ta rufe kasuwar Hausawa ta Mile 12 da Owode Onirin saboda karya dokokin muhalli.

Date:

Gwamnatin Lagos ta rufe kasuwar Hausawa ta Mile 12 da Owode Onirin saboda karya dokokin muhalli.

Gwamnatin jihar Lagos ta bayar da umarnin kulle kasuwar Hausawa ta Mile 12 da Owode Onirin a ranar Juma’a sakamakon karya dokokin muhalli.

Gwamnatin jihar Lagos ta baiwa masu gine gine a magudanan ruwa kwanaki bakwai

Cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun daraktan sashin hulda da jama’a ta ma’aikatar muhalli dake Lagos, Kunle Adeshina, ta ce an rufe kasuwannin ne biyo bayan sumamen hadin gwiwa da hukumar dake kula da abubuwan da ake zubarwa da hukumar kula (LAWMA) da tsaftar muhalli (KAI) suka kai bisa umarnin kwamishinan muhalli da albarkatun ruwa Tokunbo Wahab.

Da yake jawabi kan rufe kasuwannin Tokunbo Wahab ya ce ride kasuwae Mile 12 data Owode Onirin ya haska bukatar tabbatar da bin dokokin tsaftar muhalli a kasuwannin jihar.

Ya ce duk da cewa rufe kasuwar mataki ne mai tsauri amma yin hakan ya zama wajibi domin magance matsalolin muhalli don kare lafiyar al’umma.

Kwamishinan ya bukaci ‘yan kasuwa da masu cinikayya su rinka kulawa da muhallin su da suke gudanar da kasuwanci a koda yaushe.

Latest stories

Related stories