Saurari premier Radio
33.9 C
Kano
Saturday, May 18, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiMajalisar Dokokin Kano Ta Amince Da Kudirin Gyaran Dokar Masarautun Jihar.

Majalisar Dokokin Kano Ta Amince Da Kudirin Gyaran Dokar Masarautun Jihar.

Date:

Majalisar dokokin Kano ta amince da kudirin gyaran dokar masarautu ta jihar Kano ta shekerar 2019.

Majalisar ta amince da gyaran a zaman ta na Talatar nan karkashin kakakinta Hamisu Ibrahim Chidari.

Gyaran dai ya kunshi rage mambobin majalisar zartaswa ta sarakunan jihar Kano zuwa mutane goma sha bakwai maimakon mutane 25.

Haka kuma gyaran ya bayar da damar samar da gidajen da zasu iya gadar sarki koda Allah yayi wani sarki ya rasuwa daga cikin sarakunan Kano.

A wani cigaban kuma majalisar dokokin ta amince da sabon taken jihar Kano wanda za a rinka amfani dashi a guraren taruka a fadin jihar nan.

Gwamnatin Kano da jami’ar Bayero ne dai suka samar da taken na jihar Kano.

Majalisar ta kuma karbi takardar daga gwamnan Kano dake neman sahalewa domin samar da hukumar da zata rinka kula da tituna a yankunan karkara.

Wakilin mu Aminu Abdullahi Ibrahim ya ruwaito cewa majalisar dokokin ta Kano ta kuma karbi takarda daga gwamnan Kano dake neman majalisar ta amince da Balarabe Hassan Karaye a matsayin kwamishina a hukumar zabe ta jihar Kano (KANSIEC).

Majalisar ta kuma dage zaman ta zuwa Larabar nan.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...