Saurari premier Radio
36.9 C
Kano
Wednesday, May 8, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabarai'Yan bindiga sun sace dalibai hudu a jihar Zamfara

‘Yan bindiga sun sace dalibai hudu a jihar Zamfara

Date:

’Yan bindiga sun kai hari kan dalibai mata na Kwalejin Lafiya ta Tsafe da ke Jihar Zamfara inda suka kwashe guda 4 bayan halartar wani bikin aure.

 

Bayanai daga yankin sun ce ‘yan ta’addar sun kama wadannan dalibai ne lokacin da suke komawa Kauran-Namoda daga Birnin Magaji.

 

Lamarin ya faru ne bayan tare motocin da ke dauke da wadanda harin ya rutsa da su, inda suka kwashi matafiya 18, cikinsu har da dalibai mata 4 da wasu ’yan mata 3 da kuma wani mutum guda.

 

Shugaban Kwalejin Kula da Lafiyar, Yusuf Maradun ya tabbatar da aukuwar lamarin wanda ya ce ba’a cikin makarantar aka kwashi daliban ba.

 

Maradun ya ce lokacin da aka sace wadannan daliban makarantar na hutun karshen shekara.

 

Wani dan uwan daya daga cikin daliban ya ce ‘yan ta’addar sun bukaci fansar Naira miliyan 20 kafin sakin diyarsu.

Latest stories

Mamakon ruwa a Filato ya lalata gidaje, makarantu da asibitoci.

Wani mamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya ya...

Related stories

Mamakon ruwa a Filato ya lalata gidaje, makarantu da asibitoci.

Wani mamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya ya...