Saurari premier Radio
34.9 C
Kano
Friday, May 17, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabarai'Kidaya: Babu wanda za'a 'kirga fiye da sau 1-NPC | Premier Radio...

‘Kidaya: Babu wanda za’a ‘kirga fiye da sau 1-NPC | Premier Radio | 20.01.2023

Date:

Muhammad Bello Dabai

 

Hukumar ‘kidaya ta kasa NPC ta sanya ranar 29 ga watan Maris zuwa 1 ga watan Afrilu, domin fara ‘kidayar shekarar 2023.

 

Shugaban hukumar, Nasir Kwarra ne ya bayyana hakan ga yan jarida, bayan ganawarsa da shugaban kasa Muhammadu Buhari yau a Villa.

 

Yace hatta wadanda ba ‘yan asalin Najeriya ba, zasu shiga cikin ‘kidayar matukar suna nan a lokacin da ake aiwatar da shirin.

 

Kwarra ya kuma bayyana kwarin gwiwar cewa kidayar ta bana, zata sha banban da irin wadanda aka yi a baya, inda jami’ansu suka yi ta fama da matsalar kayan aiki.

 

Yace sabbin kayan aikin da suke da su, zasu iya daukar duk wani nau’in bayanin al’umma, da suka kunshi ‘kirgen gidaje da filaye.

 

Shugaban na NPC yace tuni aka gama rarraba yankunan ‘kidayar tsakanin jami’ansu.

 

Ga wadanda suka nemi aikin wucin gadi da hukumar kuwa, Kwarru yace kowannen su zai yi aiki ne a yankin sa, a don haka babu barazanar yin tafiya mai nisa domin zuwa aikin.

 

Ko da yake baiyi cikakken ‘karin haske kan irin matakan da suka dauka ba, yace ‘kidayar zata gudana cikin lumana, hatta a wuraren dake da matsalar tsaro.

 

Latest stories

Related stories