Saurari premier Radio
40.9 C
Kano
Wednesday, April 10, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiYa kamata CBN yayi nazari kan wa'adin karbar tsaffin kudi-NLC | Premier...

Ya kamata CBN yayi nazari kan wa’adin karbar tsaffin kudi-NLC | Premier Radio | 20.01.2023

Date:

Muhammad Bello Dabai

Kungiyar kwadago ta kasa NLC ta bukaci CBN ya sake nazari kan tabbatar da haramta tsaffin takardun naira daga 31 ga watan Janairu da muke ciki.

 

Shugaban ta na kasa, Comrade Ayuba Wabba ne yayi kiran a daidai lokacin da gwamnoni suka gana da gwamnan bankin, Godwin Emiefele akan batun.

 

Wabba yace akwai bukatar babban bankin yayi la’akari da halin da al’umma zasu shiga, musamman mazauna yankunan karkara, sabida irin asarar da zasu iya tafkawa.

Shugaban na NLC yace tun ranar 20 ga watan Disambar bara kungiyar ta kwadago ta rubuta wa gwamnan babban bankin wasika, wadda a ciki ta bayyana damuwar ta akan wannan batu na tsaida wa’adin daina amfani da tsofaffin kudi, da irin mayuwacin halin da alumma zasu shiga.

 

A nan Kano, Premier Radio ta tuntubi shugaban kungiyar Kwadago ta TUC Kwamared Mubarak Muhammad, sai dai a lokacin da aka  nemi jin ta bakinsa kan wannan kira na shugaban kungiyar Kwadago na kasa NLC, yace suna shirin shiga wata tattaunawa ta musamman kan batun.

 

A Karshen wannan wata na janairu ne dai babban bankin kasa CBN yace za’a daina amfani da tsaffin kudi na naira, 200, 500 da 1000, kuma tuni aka fara kiraye-kiraye na ganin an kara wa’adin musamman ga alummar karkara.

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories