Saurari premier Radio
26.9 C
Kano
Friday, February 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiZargin badakala: Buhari ya gana da Emefiele a Villa

Zargin badakala: Buhari ya gana da Emefiele a Villa

Date:

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin gwamnan babban bankin kasa CBN Godwin Emefiele a fadar shugaban kasa dake Abuja.

 

Wannan shine dai ganawar sa ta biyu da shugaban kasa Buhari, tun bayan dawowar gwamnan bankin daga hutun sabuwar Shekara.

 

A alhamis din nan gwamnan na CBN ya kasance a fadar shugaban kasa a cikin tawagar shugabannin bankin bunkasa tattalin arzikin kasashen larabawa karkashin jagorancin babban daraktan bankin Dakta Sidi Ould Tah.

 

A kwanakin baya Emefiele ya tafi hutun karshen Shekara, a dai-dai lokacin da aka fara bincikensa kan zargin cin hangi da rashawa tare da Dakar nauyin ‘yan ta’adda.

 

Tun da fari, wata kotu ta bawa hukumar tsaro ta DSS damar kamawa tare da bincikar gwamnan bankin, sai dai daga baya babbar kotun Tarayya dake zaune a Abuja ta yi watsi da bukatar kama Emefele .

Latest stories

Related stories