Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Monday, May 6, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiCBN ya zargi bankuna da yi masa zagon kasa

CBN ya zargi bankuna da yi masa zagon kasa

Date:

Babban Bankin kasa (CBN) ya zargi wasu bankuna da yi masa zangon kasa ta hanyar boye sabbin takardun kudade tare da ci gaba da bayar da tsofaffi.

 

Hakan na zuwa ne yayin da ya rage kwana 10 a daina amfani da tsofaffin kudaden kwata-kwata a kasar nan.

 

Babban Jami’in bankin a Jihar Ribas, Maxwell Okafor, ne ya yi zargin a Fatakwal, babban birnin Jihar lokacin da ya jagoranci ayarin CBN yayin ziyarar duba yadda bankuna da kasuwannin Jihar ke ta’ammali da sabbin kudaden a ranar Juma’a.

 

Ya ce tsakanin ranakun Alhamis da Juma’a kawai, CBN ya ba bankunan kasuwancin da ke jihar tsabar kudin da suka kai Naira biliyan hudu da rabi, inda ya nuna damuwa kan yadda har yanzu jama’a ba sa samun su.

 

Shi ma Daraktan Tsara Manufofi na bankin, Emenike Chimele, ya ce ko shakka babu wasu daga cikin bankunan na kokarin yi wa CBN zagon kasa kan sabuwar manufar.

 

Idan za a iya tunawa, CBN ya tsayar da 31 ga watan Janairun 2023 a matsayin ranar da za a daina amfani da tsofaffin kudaden kwata-kwata a Najeriya.

 

Sai dai yayin da ya rage ’yan kwanaki kafin cikar wa’adin, har yanzu mutane ma kokawa kan karancin sabbin takardun, yayin da har yanzu wasu bankunan da injinan ATM ke ci gaba da bayar da tsofaffin takardun.

Latest stories

Sarkin musulmi ya ja hankalin shugabanni kan samarwa da al’umma makoma

Mai alfarma sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na 3...

Related stories

Sarkin musulmi ya ja hankalin shugabanni kan samarwa da al’umma makoma

Mai alfarma sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na 3...