Saurari premier Radio
41.9 C
Kano
Friday, April 26, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiUmarnin Buhari rashin da'a ne ga kotun koli-El-Rufa'i | Premier Radio |...

Umarnin Buhari rashin da’a ne ga kotun koli-El-Rufa’i | Premier Radio | 17.02.2023

Date:

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa’i ya mayar da kakkausan martani kan jawabin shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda ya gabatar a kafar talabijin ta NTA a ranar Alhamis.

El-Rufa’i, ya umarci al’ummar jihar sa da su cigaba da karbar tsaffin takardun kudi na naira 500 da 1000, har sai kotun koli ta sanar da hukuncin karshe.

Ya kuma yi barazanar rufe duk wata cibiyar cinikayya da ta ki amsar tsaffin takardun, yana mai cewa yan Kaduna kar su ji tsoron kashe kudin su yadda suke so.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a jawabin kasa da ya gabatar, ya amince a cigaba da karbar takardar kudi ta naira 200, yayinda yace a kai 500 da 1000 banki domin sauyawa.

To said ai, El-Rufa’i, yace wannan umarni na shugaban kasa, rashin da’a ne ga hukuncin kotun kolin na ranar 8 ga watan Fabarairu.

Kafin yanzu, gwamnan Kaduna na daga cikin nag aba gaba wajen kare muradan gwamnatin Buhari, wanda kuma matsayar da ya dauka na yin adawa da tsarin sauya fasalin kudi, ya zo da mamaki ga masu bibiyar harkokin siyasar sa.

Latest stories

Related stories