33.9 C
Kano
Tuesday, May 7, 2024
HomeLabaraiKarancin sabon kudi  ba zai hana zabe ba-INEC

Karancin sabon kudi  ba zai hana zabe ba-INEC

Date:

Hukumar zabe ta kasa INEC ta ce karancin sabon kudi da ake fuskanta ba zai hana gudanar da zabuka ba.

Shugaban hukumar Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana hakan  yayin duba yadda ake horas da ma’aikatan wucin gadi na INEC a Abuja. 

A cewar shugaban hukumar ba dukkan ayyukan da za a gudanar a lokacin zabe ke bukatar tsabar kudi ba, don haka karancin sabon kudi ba zai bada matsala ba.

Hakan na zuwa ne daidai lokacin da ake ta rade-radin cewa za a iya dage zaben sakamakon karancin kudi da ake fuskanta, biyo bayan sauya fasalin kudi da babban bankin Najeriya ya yi.

Shugaban na INEC ya jaddada cewa hukumar ta shirya tsaf domin gudanar da zabukan shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya a ranar Asabar 25 ga watan Fabrairu. 

Ya kuma bayyana jin dadinsa da ci gaban da aka samu ya zuwa yanzu, inda ya bada tabbacin cewa a mako mai zuwa, ‘yan Nijeriya za su kada kuri’a a rumfunan zabe sama da 176,000 domin gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya.

Latest stories

Related stories