27.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabaraiWasanniUEFA Super Cup:Real Madrid na shirin fafatawa da Frankfurt

UEFA Super Cup:Real Madrid na shirin fafatawa da Frankfurt

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid na shirin buga wasan karshe da Eintracht Frankfurt a gasar UEFA Super Cup.

 

Kungiyoyi biyun zasu buga wasan karshen a filin wasa na Olympic dake birnin Helsinki na kasar Finland a daren Larabar nan.

 

Gasar ta Super Cup ta shekarar 2022 itace karo na 47 jumulla, inda Chelsea itace wadda ta lashe a gasar bara data gabata.

 

Wannan gasa dai ana shiryata ga kungiyoyi biyun da suka lashe manyan gasa a nahiyar turai.

 

Wato Real Madrid data lashe gasar cin kofin turai Champions League, bayan doke Liverpool a wasan karshe.

 

Ita kuma Eintracht Frankfurt ita ce ta lashe gasar Europa ta shekarar da ta gabata.

 

Yanzu haka dai ana saran Real Madrid Ka iya amfani da wasu cikin wannan jerin ‘Yan wasan domin buga fafatwar Larabar nan.

 

Inda ake Saran Carlo Ancelloti zai amfani da Thibaut Courtois; Dani Carvajal, Eder Militao, David Alaba, Benjamin Mendy; Toni Kroos, Casemiro, Luka Modric; Fede Valverde, Karim Benzema, Vinicius Junior.

 

Sai kuma kungiyar kwallon kafa ta Eintracht Frankfurt ka iya amfani da Kevin Trapp; Almany Toure, Tuta, Evan N’Dicka; Ansgar Knauff, Moussa Sow, Sebastian Rode, Christopher Lenz; Daichi Kamada, Mario Gotze, Rafael Borre.

 

Alkalin wasa Michael Oliver dan kasar Ingila dai shine zai jaboranci wasan karshen da zai gudana a ranar Larabar nan 10 ga Agustan 2022.

Latest stories