Saurari premier Radio
24.9 C
Kano
Friday, April 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiWasanniReal Madrid ta lashe Super Cup Karo na biyar

Real Madrid ta lashe Super Cup Karo na biyar

Date:

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta lashe gasar cin kofin gwani na gwanaye na UEFA Super Cup, bayan doke Eintracht Frankfurt a wasan karshe a ranar Larabar nan da ci 2-0.

 

Katafaren filin wasa na Olympic dake birnin Helsinki na kasar Finland ne ya karbi bakuncin fafatawar data gudana a daren Larabar 10 ga Agusta.

 

Alkalin wasa Michael Oliver dan kasar Ingila dai shine ya jaboranci wasan karshen da kungiyoyin kasar Spain da Jamus suka fafata.

 

Dan wasa David Alaba ne dai ya fara zura kwallon farko a wasan a minti na 38, bayan samun tai mako daga hannun Casemiro.

 

Sai kuma dan wasa Karim Benzema da ya kara kwallo ta biyu a minti na 65, bayan samun tai mako daga Vinicius Junior.

 

Gasar Super Cup ta shekarar 2022, itace karo na 47 jumulla, da Kawo yanzu Madrid ta lashe gasar sau biyar a tarihi a shekarun 2002, 2014, 2016 da kuma 2017.

 

Hakan da ke nuna yadda Madrid ta kamo Barcelona da AC Milan a yawan lashe gasar ta Super Cup.

Wannan gasa dai ana shiryata ga kungiyoyi biyun da suka lashe manyan gasa a nahiyar turai.

 

Wato Real Madrid data lashe gasar cin kofin turai Champions League, bayan doke Liverpool a wasan karshe.

 

Sai kuma Eintracht Frankfurt data ta lashe gasar Europa ta shekarar da ta gabata bayan doke Rangers.

Latest stories

Dan Ganduje ya kai wa Muhuyi ziyarar goyan bayan a binciki mahaifansa

Dan tsohon gwamnan Kano, Abdulaziz Abdullahi Ganduje, ya kai...

Farashin Dizel ya koma 1000 a Najeriya

Rahotanni sun bayyana matatar mai ta Dangote ta sanar...

Related stories

AFCON 2023: Kashim Shettima ya tafi Cote d’Ivoire don marawa Super Eagles baya

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, ya bar Najeriya zuwa...