Ahmad Hamisu Gwale
A ranar Asabar dinnan, 13 ga Agusta 2022, an buga wasanni da dama a nahiyar turai, kama daga kasar Ingila, Sipaniya, Faransa da kuma Italiya.
A Faransa PSG tayi nasarar doke Montpellier da ci 5-2 a wasan da suka fafata.
Dan wasa Neymar JR dai ya zura kwallo biyu a wasan a minti na 42 da 50, sai dan wasa Sacko ya zura kwallo a raga wato Own goal a minti na 38.
Sai kuma Mbappe ya zura kwallo a minti na 68, inda shima
Renato Sanches ya zura a minti na 86.
Daga bangaren Montpellier kuwa ‘yan wasa Khazri da Enzo Tchato ne suka zura kwallo a minti na 57 da 90.
Daga kasar Ingila kuwa Brentford ta lallasa Manchester United da ci 4-0 a wasan mako na biyu na gasar Firimiya da suka fafata.
Kwallayen da dan wasa
J. Dasilva ya zura a minti na 9, sai
M. Jensen ya zura a minti na 17
da Mee ya zura a minti na 29 da kuma B. Mbeumo a minti na 34.
Haka zalika Arsenal ta lallasa Leicester City da ci 4-2 a ranar Asabar dinnan.
‘Yan wasan Arsenal da suka zura kwallo sun hada da Jesus a minti na 22 da 34, sai Xhaka a minti na 54 da kuma Martinelli 74.
Daga Leicester City kuwa dan wasa W. Saliba ya zura kwallo a ragarsu wato OG a minti na 54 shima Maddison ya zura a minti na 73.
Ita ma Manchester City ta lallasa
Bournemouth da ci 4-0 a karawar da suka fafata.
Gundogan ya zura kwallo a minti na 18, De Bruyne a minti na 30
Foden a minti na 36 da kuma
Lerma a minti na 78 wato OG.
Daga La Liga ta kasar Spain kuwa a wasan farko na gasar Barcelona da Rayo Vallecano sun tashi wasa 0-0.
A Italiya a gasar Serie A kuwa Inter Milan tayi nasara akan
Lecce da ci 1-2.
Kwallayen da Lukaku ya zura a minti na 1 sai dan wasa Dumfries ya zura kwallo shima a minti na 90.
Daga bangaren Lecce kuwa dan wasa A. Ceesay ne ya zura kwallo daya tilo a minti na 47.
Duka fafatawar dai na kakar wasannin shekarar 2022/2023 wanda ake ci gaba gudanar wa a kasashe daban-daban da suke a nahiyar turai.