Saurari premier Radio
23.9 C
Kano
Saturday, February 24, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiWasanniYadda manyan kungiyoyi a turai suka buga wasa a ranar Asabar

Yadda manyan kungiyoyi a turai suka buga wasa a ranar Asabar

Date:

A ranar Asabar dinnan, 13 ga Agusta 2022, an buga wasanni da dama a nahiyar turai, kama daga kasar Ingila, Sipaniya, Faransa da kuma Italiya.

 

A Faransa PSG tayi nasarar doke Montpellier da ci 5-2 a wasan da suka fafata.

 

Dan wasa Neymar JR dai ya zura kwallo biyu a wasan a minti na 42 da 50, sai dan wasa Sacko ya zura kwallo a raga wato Own goal a minti na 38.

 

Sai kuma Mbappe ya zura kwallo a minti na 68, inda shima Renato Sanches ya zura a minti na 86.

 

Daga bangaren Montpellier kuwa ‘yan wasa Khazri da Enzo Tchato ne suka zura kwallo a minti na 57 da 90.

 

Daga kasar Ingila kuwa Brentford ta lallasa Manchester United da ci 4-0 a wasan mako na biyu na gasar Firimiya da suka fafata.

 

Kwallayen da dan wasa J. Dasilva ya zura a minti na 9, sai M. Jensen ya zura a minti na 17 da Mee ya zura a minti na 29 da kuma B. Mbeumo a minti na 34.

 

Haka zalika Arsenal ta lallasa Leicester City da ci 4-2 a ranar Asabar dinnan.

 

‘Yan wasan Arsenal da suka zura kwallo sun hada da Jesus a minti na 22 da 34, sai Xhaka a minti na 54 da kuma Martinelli 74.

 

Daga Leicester City kuwa dan wasa W. Saliba ya zura kwallo a ragarsu wato OG a minti na 54 shima Maddison ya zura a minti na 73.

 

Ita ma Manchester City ta lallasa Bournemouth da ci 4-0 a karawar da suka fafata.

 

Gundogan ya zura kwallo a minti na 18, De Bruyne a minti na 30 Foden a minti na 36 da kuma Lerma a minti na 78 wato OG.

 

Daga La Liga ta kasar Spain kuwa a wasan farko na gasar Barcelona da Rayo Vallecano sun tashi wasa 0-0.

 

A Italiya a gasar Serie A kuwa Inter Milan tayi nasara akan Lecce da ci 1-2.

 

Kwallayen da Lukaku ya zura a minti na 1 sai dan wasa Dumfries ya zura kwallo shima a minti na 90.

 

Daga bangaren Lecce kuwa dan wasa A. Ceesay ne ya zura kwallo daya tilo a minti na 47.

 

Duka fafatawar dai na kakar wasannin shekarar 2022/2023 wanda ake ci gaba gudanar wa a kasashe daban-daban da suke a nahiyar turai.

Latest stories

Related stories

AFCON 2023: Kashim Shettima ya tafi Cote d’Ivoire don marawa Super Eagles baya

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, ya bar Najeriya zuwa...