Saurari premier Radio
26.9 C
Kano
Friday, February 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiWasanniKo Manchester United na shirin maimaita tarihin kakar 1993 a gasar Firimiya?

Ko Manchester United na shirin maimaita tarihin kakar 1993 a gasar Firimiya?

Date:

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United na ci gaba da samun koma baya a sabuwar kakar wasannin shekarar 2022/2023 wadda aka fara a watan Agustan da muke ciki.

 

Inda Kungiyar ta United a wasan farko da ta buga da Brighton tayi rashin nasara da ci 2-1 a wasan da ya gudana a filin wasa na Old Trafford a ranar 7 ga Agusta.

 

Sai kuma a ranar 13 ga watan na Agusta a wasan mako na biyu na gasar, Brenford ta sake lallasa Manchester United da ci 4-0 da nema.

 

Lamarin da kawo yanzu kungiyar na matakin karshe wato ta 20 a wasanni biyu da aka buga kuma ba tada maki ko daya.

 

To sai dai Manchester United ta yi irin wannan rashin nasara a wasannin biyun farko a kakar shekarar 1992/1993 karkashin jagorancin tsowon Mai horar wa Sir Alex Ferguson.

 

'Yan wasan Manchester United Varane da Cristiano Ronaldo
Yan wasan Manchester United Varane da Cristiano Ronaldo

Inda a wasan farko sukai rashin nasara da ci 1-2 a hannun Sheffield United.

 

Sai kuma wasa na biyu aka kara cinsu da ci 3-0 wanda Everton suka cisu har gida.

 

Amma daga bisani Manchester United a wannan shekara ta lashe gasar ta Firimiya a karon farko a tarihi, inda ta bada ta zarar maki 10 tsakaninta da Aston Villa wadda ta kammala a mataki na biyu.

 

Yanzu haka dai a iya cewa lokaci ne kadai ka iya tabbatar da ko United zata iya maimaita tarihin ko kuma aka sin haka? Lokaci ne dai kawai zai iya tantancewa.

 

Kawo yanzu dai a mako mai zuwa wato ranar 22 ga watan da muke ciki, Manchester United zata kece raini da Liverpool a wasan hamayya na mako na uku a gasar ta Firimiyar kasar Ingila.http://Manchester United

Latest stories

Related stories

AFCON 2023: Kashim Shettima ya tafi Cote d’Ivoire don marawa Super Eagles baya

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, ya bar Najeriya zuwa...