Saurari premier Radio
41.9 C
Kano
Friday, April 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiWasanniSalah ya ba da gudunmawar dala 156,000 don sake gina Coci a...

Salah ya ba da gudunmawar dala 156,000 don sake gina Coci a Masar

Date:

Kyaftin din kasar kasar Masar kuma dan wasa a Liverpool Muhammad Salah, ya bayar da gudunmawar Dalar amurka 156,000, kwatankwacin fam miliyan 3 na kudin kasar Masar.

 

 

Gudunmawar kudin na zuwa ne bayan da a ranar Litinin gobara ta rutsa da ginin wata coci a kasar wanda ya hada da mutane 41, ciki har da  yara 10 wanda suka rasa rayukansu.

 

 

Gobarar wadda ta tashi a cocin  Abu Sefein da ke yankin Giza na kasar ta Masar.

 

 

Rahotanni dai sun bayyana a ranar Lahadin data gabata mutane 41 gobarar ta kashe, Kuma 14 suka jukkata a lokacin.

 

Wasu cikin masu makoki a kofar Coci.
Wasu cikin masu makoki a kofar Cocin

 

 

Tuni dai dan wasa Salah ya jajanta wa wadanda suka mutu a cocin ta shafinsa na Twitter, sa’o’i kadan bayan faruwar lamarin.

 

 

Inda ya wallafa cewa  “Ina mika ta’aziyyata ga wadanda suka mutu a Cocin Abu Sefein, tare da fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata.”

 

 

Tuni dai shafin sada zumunta na  kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ya nuna alhini ga wadanda gobarar cocin ta shafa a Masar.

 

 

Inda itama hukumar kwallon kafa ta Masar ta mika ta’aziyya ga wadanda gobarar cocin Giza ta shafa.

 

 

Cikin binciken da aka gudanar ya nuna cewa gobarar wutar lantarki ta mamaye cocin Abu Sefein da ke Imbaba, wani gunduma mai aiki a yammacin kogin Nilu, wani yanki na yankin Giza a babban birnin Alkahira na Masar.

Latest stories

NPFL: Gwamnatin Kano ta bawa Kano Pillars wasa Uku domin ta yi Nasara

Gwamnatin Jihar Kano ta bawa kungiyar Kwallon kafa ta...

Dan Ganduje ya kai wa Muhuyi ziyarar goyan bayan a binciki mahaifansa

Dan tsohon gwamnan Kano, Abdulaziz Abdullahi Ganduje, ya kai...

Related stories