Saurari premier Radio
31.9 C
Kano
Thursday, April 18, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiMajalisar dokokin Kano za tayi bincike akan Kano Pillars

Majalisar dokokin Kano za tayi bincike akan Kano Pillars

Date:

Majalisar dokokin Kano ta kafa kwamitin bincike kan dabbarwar da ta dabai baye kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars.

 

Dan majalisar jiha mai wakiltar Rano, ne ya gabatar da kudirin don daukar mataki kan koma bayan da kungiyar ke fuskanta a baya bayan nan.

 

Yayin zaman majalisar na Litinin din nan ta amince da baiwa kwamitin wasanni karkashin shugaban kwamitin Nuradeen Alhassan, don yin bincike tare da gabatar da rahoto kan matsalolin kungiyar ta Kano Pillars ke ciki nan da makonni biyu.

Shugaban majalisar dokokin Kano: Iyaye su rinka sanya ido akan ‘ya’yan su

A dai zaman majalisar na Litinin din nan gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya bukaci majalisar dokokin tayi gyara kan dokar masu bukata ta musamman da ta kula da inganci abinci da magunguna ta jihar nan don tafiya dai dai da zamani.

Shugaban majalisar Injiniya Hamisu Ibrahim Chidari, ne ya karanta takardar neman yin gyaran.

 

Haka zalika gwamnan ya kuma bukaci majalisar ta amince da Alkali Ibrahim Umar mai ritaya da Jamila Sani Garko, a matsayin mambobi a hukumar shari’a ta jihar Kano.

 

Majalisar ta baiwa kwamitin shari’a daya tantance sunayen tare da gabatar da rahoton sa a ranar Laraba mai zuwa.
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya kuma bukaci majalisar dokokin ta amince da sauyawa Jami’ar kimiya da fasaha ta garin Wudil suna zuwa Aliko Dangote University Of Science and Technology.

 

Wannan na kunshe ne cikin takardar da gwamnan ya aikewa majalisar a zamanta na Litinin din nan.

 

Idan za a iya tunawa dai tun a ranar 16 ga watan Mayun shekarar da muke ciki ne majalisar zartaswa ta amince da sauyawa jami’ar suna zuwa Aliko Dangode.

 

Gwamnatin ta sauyawa jami’ar suna ne bisa irin gudunmawar da Alhaji Aliko Dangote, ke baiwa ilimi a jihar nan da kasa baki daya.

 

Alhaji Aliko Dangote, dai shine uban jami’ar ta Wudil kuma bakar fata wanda yafi kowa kudi a nahiyar afurka.

Latest stories

Farashin Dizel ya koma 1000 a Najeriya

Rahotanni sun bayyana matatar mai ta Dangote ta sanar...

Related stories

Farashin Dizel ya koma 1000 a Najeriya

Rahotanni sun bayyana matatar mai ta Dangote ta sanar...