Saurari premier Radio
23.9 C
Kano
Friday, February 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiShugaban majalisar dokokin Kano: Iyaye su rinka sanya ido akan 'ya'yan su

Shugaban majalisar dokokin Kano: Iyaye su rinka sanya ido akan ‘ya’yan su

Date:

Aminu Abdullahi Ibrahim

 

Shugaban majalisar dokokin Kano Injiniya Hamisu Ibrahim Chidari, yayi kira ga iyaye dasu rinka sanya ido kan zirga-zirgar ‘ya’yan su.

 

Wannan na kunshe ne cikin sanarwar da daraktan yada labarai na majalisar Uba Abdullahi, ya fitar a Asabar din nan.

 

Abinda yasa bamu amince da dokar kananan yara ba-Cidari

Shugaban yayi kiranne a sakonsa na murnar shigowa sabuwar shekarar musulunci ta 1444, inda ya bukaci iyaye dasu rinka baiwa ‘ya’yan su shawarwarin da suka dace domin bunkasa dabi’un su a lokacin samartakar.

 

Injiniya Hamisu Ibrahim Chidari, ya yabawa malamai da limamai bisa addu’o’in da suke ga kasar nan don ganin ta fita daga halin kuncin da take ciki.

 

Haka zalika ya yabawa gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, tare da taya al’ummar Danbatta da Makoda murnar shigowa sabuwar shekarar.

Latest stories

Related stories