30.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabaraiHajj: Rukunin farko na Alhazan Kano sun dawo gida

Hajj: Rukunin farko na Alhazan Kano sun dawo gida

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Ahmad Hamisu Gwale

Rukunin farko na Mahajjatan Kano 259 sun dawo Kano daga kasa mai tsarki bayan sauke faralin a bana.

Mahajjatan kanan hukumomin Rano, Bunkure da Kura ne dai jirgin farko da hukumar jin dadin alhazai ta kasa tayi jigilar su zuwa nan Kano a ranar Juma’ar nan.

Alhazan da suka hau jirgin AZMAN mai lamba ZQ2349 sun isa filin jirgin saman Malam Aminu Kano da misalin karfe 02:41 na rana.

Babban Sakataren Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Muhammed Abba-Danbatta ne ya bayyana hakan ga manema labarai.

Muhammad Abba Danbatta ya ce  alhazan sun kasance masu biyayya da bin doka a kasa mai tsarki.

Ya ce  ana sa ran dawowar kashi na biyu na maniyyata nan gaba kadan.

Latest stories