33.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabaraiKasuwanciKamfanonin jiragen saman kasar nan sun kara kudin tafiye-tafiye.

Kamfanonin jiragen saman kasar nan sun kara kudin tafiye-tafiye.

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Kamfanonin jiragen saman kasar nan sun kara kudin tafiye-tafiye.

 

Kamfanonin jiragen sama na kasar nan sun kara kudin jirgi daga Lagos zuwa Abuja sakamakon tashin farashin man jirgi.

 

A labarin da Peoples Gazette, ta wallafa ya nuna cewa jirgin Air Peace sun saida tikitin Lagos zuwa Abuja akan naira dubu dari (N100,000.) daga karfe 10:40 a.m. zuwa 7:50 p.m.

 

Jirgin Max Air sun saida nasu Tikitin naira dubu dari da ashirin da biyar (N125,000) da naira dubu dari da talata (130,000,).

 

Kujerar jirgin Air Peace an saida ita a ranar Lahadi akan kudi naira dubu tamanin da biyar N85,000, Max Air sun cigaba da sayar da tikitin kujera akan naira dubu N84,000 da naira N75,000.

Rikincin Russia da Ukraine zai kawo tsadar Gurasa da Burodi a Kano

Yayin da tikitin kujerar Arik aka cigaba da sayar dashi akan kudi naira N80,595 da 93,452.

 

Ana danganta karin kudin jirgin da matsalolin da suka dabai baye harkokin sufurin jiragen saman kasar nan ciki harda faduwar darajar naira da karin farashin man jirgi.

Ba mu fara karbar kudin aikin hajjin bana ba inji hukumar alhazai

Idan za a iya tunawa dai a watan Mayun da yagabata ne kamfanonin jiragen sukayi barazanar tsaida ayyukansu sakamakon karuwar farashin man jirgi daga 160 zuwa 900 duk lita daya.

Latest stories