Saurari premier Radio
32.9 C
Kano
Saturday, April 20, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiRikincin Russia da Ukraine zai kawo tsadar Gurasa da Burodi a Kano

Rikincin Russia da Ukraine zai kawo tsadar Gurasa da Burodi a Kano

Date:

Mukhtar Yahya Usman

Akwai yiwuwar rikicin da ake fama da shi tsakanin kasashen Rasha da Ukraine ya sa farashin burodi da na gurasa ya yi tashin gwauron zabo a Kano dama kasa baki daya.

Burodi da gurasa na daya daga cikin abincin da aka fi amfani da su a gidajen ’yan Najeriya da dama; ba talaka ba mai kudi.

Rasha dai ita ce kasar da ta fi kowace kasa fitar da alkama a duniya, inda take samar da sama da kaso 18 cikin 100 na alkamar da ake amfani da ita a duniya.

Hakan dai na nufin muddin yakin ya shafi samar da alkamar a kasar, akwai yiwuwar farashinta ya karu a kasuwannin duniya, ciki har da na Najeriya, lamarin da ka iya haifar da karin kudin duk wani dangin abincin da ake sarrafawa daga alkamar.

A tsakanin shekarar 2020 zuwa 2021 dai, farashin burodi ya karu da sama da kaso 80 cikin 100 a Najeriya.

Babban Bankin Najeriya (CBN), ya ce alkama ita ce abinci na uku da aka fi amfani da shi a kasar nan, yayin da kasar nan ke iya noma kaso daya cikin 100 kacal.

Haka kuma ragowar kaso 99, ake shigo da su daga ketare.

Hakan dai ya sa Najeriya kashe sama da Dalar Amurka biliyan biyu a kowace shekara wajen shigo da alkama daga kasashen waje.

A shekarar 2019 kadai, Rasha da Ukraine sun samar da daya bisa hudu na alkamar da aka yi amfani da ita a fadin duniya, kamar yadda Cibiyar sa ido kan Harkokin Tattalin Arziki (OEC) ta tabbatar.

Tuni dai Kungiyar Masu Gasa Burodi ta Najeriya (AMBCN) ta ce babu makawa yanayin zai kara farashin burodin a Najeriya kowane lokaci daga yanzu

Latest stories

NPFL: Gwamnatin Kano ta bawa Kano Pillars wasa Uku domin ta yi Nasara

Gwamnatin Jihar Kano ta bawa kungiyar Kwallon kafa ta...

Dan Ganduje ya kai wa Muhuyi ziyarar goyan bayan a binciki mahaifansa

Dan tsohon gwamnan Kano, Abdulaziz Abdullahi Ganduje, ya kai...

Related stories

Dan Ganduje ya kai wa Muhuyi ziyarar goyan bayan a binciki mahaifansa

Dan tsohon gwamnan Kano, Abdulaziz Abdullahi Ganduje, ya kai...

Farashin Dizel ya koma 1000 a Najeriya

Rahotanni sun bayyana matatar mai ta Dangote ta sanar...