Saurari premier Radio
27.9 C
Kano
Sunday, April 14, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKotu a Kano ta ci tarar KAROTA kan kama masu goyo a...

Kotu a Kano ta ci tarar KAROTA kan kama masu goyo a babur

Date:

Abubakar Haruna Galadanci

Babbar kotun jiha da ke Bompai a nan Kano ta umarci hukumar KAROTA ta biya wasu mutun uku N500,000 kowannensu bayan da hukumar ta kamasu da zargin yin goyo a baburansu.

Alkalin kotun mai shari’a Nasiru Saminu ya ce a yanzu yin goyo a babur ba laifi bane a dokar kasa, matukar ba haya suke yi da baburanba.

Watanni 18 ke nan da wasu mutane tara suka shigar da karar hukumar ta KAROTA gaban koton, bisa kamasu da suka yi don kawai sun dauko iyalansu a bayan baburansu.

Bayan da aka shafe tsahon lokaci ana tafka shari’ar, alkalin ya yanke hukunci cewar hukumar KAROTA ta aikata laifi da ta kama mutanen kuma ta umarceta da ta biya su diyya.

Koton ta umarci a biya mutane ukun farko diyyar N500,000 kowanne kan kamasu da aka yi ba bisa ka’ida ba, sai kuma wata N100,000 kan bata musu lokaci.

Haka kuma ragowar mutane shidan aka hakurkurtar da su tare da tabbatar da anyi musu laifi.

Jimkadan bayan yanke hukuncin ne lauyan wanda ke kare masu korafin  Barrister Abdulkareem Kabir Maude ya ce kotu ta tabbatar da cewa kowa zai iya goyo a kan baburinsa.

Ya ce kotu ta yi umarnin a dowowa da wanda aka ci tara kudadensu da aka karba kuma a biya su diyya.

“Kamasun da aka yi da kuma kudaden da aka karba a hannunsu ya sabawa doka da kuma kwanstitushin na kasar nan.

“Kotu ta ce a dawo musu da kudadensu da aka karba, mutane ukun farko a biya su dubu 500 kowannensu, a kuma biya su kudin kara N100,000.

“Kotu ta kuma ja kunnen shugaban hukumar KAROTA Bappa Babba Dan Agundi da ya sani dokace ta kafa shi, tunda doka ce ta kafashi dole ya bi doka da duk irin dokokin da suka kafa wannan gida.” A cewarsa.

Shima guda cikin wadanda suka samu Nasara a kotun Bello Basi Fagge ya ce sunyi farinciki da hukuncin kotun.

Ya ce wannan wata ‘yar manuniya ce ga dukkanin jami’an tsaro cewa doka na aikin akan kowa.

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories