Saurari premier Radio
40.5 C
Kano
Sunday, May 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKAROTA ta kama barayin da ke amfani da dan Sahu wajen satar...

KAROTA ta kama barayin da ke amfani da dan Sahu wajen satar wayoyin jama’a

Date:

Mukhtar Yahya Usman

Hukumar KAROTA tacafke wani matukin Adai-daita Sahu Abdullahi Babakura bisa zargin yin amfanin da dan sahunsa wajen satar wayoyin jama’a.

Wanann na kunshe cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar Nabilusi Abubakar Kofar Na’isa ya fitar ranar Litinin.

Kofar Na’isa ya ce matashin dan asalin garin Maiduguri ne da yake sana’ar Adadidaita Sahu a Kano.

Ya ce jami’in hukumar ne suka kamashi a bakin tashar motar ‘Yankaba ranar Asabar din da ta gabata jim kadan bayan wani magidanci ya nemi taimakon jami’an hukumar kan dan sahun.

Magidancin ya ce bayan saukarsa daga Adai-daita Sahun mutumin ne ya fahimci sun dauke masa yawarsa ya yin da ya ke cikin baburin.

Shaka kuma da jami’an KAROTA suka cafke shi sun same shi da wayoyi guda uku kirar androad.

A binciken da Hukumar KAROTA ta gudanar ta gano Babakura na amfani da shigowar baki da ke sauka a tashar  motar Yankaba domin aikata muguwar sana’arsa.

Idan sun bukaci ya kai  su waje sai ya dauke su, da zarar sun dauke wayar mutum sai su ce masa ya sauka ba nan za su yi ba, kamar yadda suka yi wa wani magidanci mai suna Lawan Abdulkarim lokacin da  ya dawo daga tafiya.

Wani shi ma da suka yi masa irin haka makwanni biyu da suka gabata ya bayyana wa Hukumar KAROTA  irin dabarun da suke yin amfani da su kafin sace wayar.

Abdullahi Babakura ya bayyanawa Hukumar cewa ba shi kadai yake yin wannan mummunar ta’adar ba, suna yi ne tare da wani abokinsa mai suna Ibrahim Aliyos Kwaya dan unguwar Gama.

Tini dai Hukumar  ta mika shi ga rundunar’ Yansanta ta jihar Kano domin fadada bincike.

Ko a kwanakin baya ma jami’an hukumar sun cafke wani matashi bisa zargin satar wayoyida kayan jama’a.

Shugaban Hukumar Baffa Babba Dan Agundi na kara kira ga jama’a da su dinga kula da kayayyakinsu, musamman idan sun hau Adaidaita Sahu, saboda sabbin dabarun da bata-garin matukan ke amfani da su wajen raba jama’a da kayayyakinsu.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...