Saurari premier Radio
24.8 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiAna fargabar hadarin mota ya kashe mutum 11 a Kano

Ana fargabar hadarin mota ya kashe mutum 11 a Kano

Date:

Mukhtar Yahya Usman

Ana fargabar mutuwar mutane 11 wasu hudu suka jikkata a wani mummunan hadarin mota da ya afku a garin Tsamiya da ke karamar hukumar Kura a nan Kano.

Shaidun gani da ido sunce hadarin ya faru ne da misalign karfe 3:30 na yammacin yau Litinin.

A cewarsu wata motar dakon kaya ta kamfanin Dangote ce ta haddasa hadarin.

Wani shaidar gani da ido Umar Sani ya ce motoci ne biyu kirar Hayis da J5 suka yi taho mu gama.

Ya ce motar Dangoten ce ke gudun wuce sa’a ta dannesu lokacin da take kokarin wucewa da gaggawa.

Har yanzu ana ci gaba da zakulo wadanda suka mutu da wadanda suka yi rauni a cikin motocin.

Muntuntubi jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta Jihar Kano ba mu sameshi ba amma dai za mu ci gaba da bibiyarsa.

Latest stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

Related stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...