Gwamnatin tarayya ta haramta shigo da layukan waya (SIM CARDS) kasar nan.
Ministan sadarwa da tattalin arziki na zamani Isah Ali Pantami, ne ya bayyana haka a jihar Lagos yayin wani taro da ma’aikatar sadarwa ta kasa ta shirya.
Gwamnatin tarayya za ta siyawa NDLEA motocin kama masu shan kwaya
Pantami, ya ce babbar kasa a afurka bai kamata ta rinka shigo da kayan da zata iya samarwa da kanta ba.
“Bari na bayyana muku a fili gwamnatin tarayya ba zata yadda da cigaba da shigo da layukan waya ba. Muna samar dasu yanzu a cikin kasar nan.
Gwamnatin tarayya na duba yiwuwar haramta acaba a kasar nan
” Burin mu shine mu bunkasa abubuwan cikin gida a bangaren sadarwa ta yadda daga shekarar 2025 zamu dogara da kanmu da kaso 80; a cewar Pantami.
Ya bukaci masu ruwa da tsaki da alummar kasar nan su goyawa gwamnati baya wajen bunkasa abubuwan da ake samarwa a cikin gida.
“Idan mukayi haka tarihi zai zama mai kyau a gare mu,” inji shi.
A watan Yuni da yagabata Pantami, ya bayyana cewa gwamnatin shugaba Buhari ta samar da ma’aikatar kera layukan waya a jihar Lagos.
Ya ce kayan aiki da ginin da akayi da hadin gwiwar kamfani mai zaman kansa zai iya samar da layukan waya miliyan 200 a kowace shekara wadanda kuma za a iya fitar dasu zuwa wasu kasashen afurka.