Saurari premier Radio
40.5 C
Kano
Sunday, May 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin tarayya na duba yiwuwar haramta acaba a kasar nan

Gwamnatin tarayya na duba yiwuwar haramta acaba a kasar nan

Date:

Aminu Abdullahi

Gwamnatin tarayya ta ce ta fara duba yiwuwar hana sana’ar Achaba a fadin kasar nan.

Ministan shari’a Abubakar Malami ne ya sanar da haka ranar Alhamis, jim kadan da bayan kammala taron Majalisar Tsaro ta Kasa wanda Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta.

Ministan ya ce bincike ya nuna cewa ana amfani da Achaba wajen harkar ma’adainai ba bisa ka’ida ba.

Adon haka ya ce hanawar zai katse hanyoyin da ‘yan ta’adda da ‘yan fashin daji ke samun kudi.

Malami ya ce ‘yan ta’adda na amfani da babura domin yin zirga-zirga yayinda kuma suke samun kudin siyan makamai ta hanyar hakar ma’adanai.

Dangane da illar da hakan zai haifar kuwa Abubakar Malami, ya ce gwamnatin tarayya za ta sanya ra’ayin alumma akan gaba.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...