33.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabaraiYadda ruwan sama ya fara hallaka muta ne a Kano

Yadda ruwan sama ya fara hallaka muta ne a Kano

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Mukhtar Yahya Usman

An samu gawar wata budurwa da ba ta wuce shekaru 15 ba da ruwa ya cinye a cikin kwata a shatale talen dangi da ke nan Kano.

An sami gawar ta ne ya yin da ake laluben wani mai mashi da yaransa da ya fada cikin kwatar da ke gefen gadar da ake kyautata zanto ruwa ya tafi da su.

Sai dai maimakon samun mai baburin da yaran, sai aka gano gawar yarinyar ruwa ya taho da ita daga wani wuri.

A cewar jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Kano SP Abdullahi Haruna Kiya, har yanzu ba a san daga ina budurwar ta fito ba.

Ya ce ofishin ‘yan sanda na yankin ne suka ba da rahoton tsintar gawar , ida ya ce har yanzu ana  neman iyayenta.

Haka kuma ya ce har yanzu ba aji duriyar wadanda ake neman ba, da alama ruwa suma ya cinyesu.

a yammacin jiya Lahadi ne dai aka samu mamakon ruwan sama da ya cinye unguwanni da dama tare da haddasa rushewar gidaje da kuma salwantar rayukan jama’a.

Latest stories