Abdurrashid Hussain
Hukumar kula da yanayi ta kasa NIMET ta yi hasashen samun yanayin hadari da ruwan sama daga ranar Litinin zuwa Laraba.
Sakamakon hasashen yanayin da NIMET ta fitar a Abuja ya nuna cewa za a yi ruwan sama kamar da bakin kwarya da sanyin safiya a Jihohin Sokoto, Zamfara, Kebbi da Katsina.
Za kuma a samu ruwan da rana a wasu sassan Bauchi, Kaduna da Taraba.
NIMET ta kuma yi hasashen cewa sararin samaniya a ranar Talata zai kasance cikin yanayin hasken rana jefi-jefi a yankin arewacin kasar nan da yiwuwar samun tsawa a sassan jihar Taraba da safe.
Yayin da ake sa ran samun tsawa a wasu sassan jihohin Kebbi, Zamfara, Sokoto, Kaduna, Kano, Borno, Gombe, Adamawa da Taraba da yammacin ranar.