37.6 C
Kano
Saturday, June 3, 2023
HomeLabaraiKano: ‘Yan sanda sun kama kwayar Tramadol ta naira miliyan 25

Kano: ‘Yan sanda sun kama kwayar Tramadol ta naira miliyan 25

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano ta kama wani mutum mai suna Abba Musa dauke da kwayar Tramadol wadda darajarta ta kai naira miliyan 25.

An kama wanda ake zargin mai shekaru 30, da fakitin Tramadol guda 500, a ranar 31 ga watan Yuni da misalin karfe 10:30 na dare a kan titin Ahmadu Bello a cikin wata mota kirar Honda Accord 2016.

Binciken da rundunar ta gudanar ya nuna cewa wanda ake zargin ya bayyana cewa motar mallakin wani abokin sa ne mai suna  Sulaiman Danwawu mazaunin unguwar Rijiyar Zaki.

A cewar sanarwa da kakakin rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar rundunar ta yi nasarar kama mai motar, inda ya tabbatar da cewa ya tawo da kwayar ne daga Onitsha dake jihar Anambra domin siyar da ita a jihar Kano.

Tuni dai mataimakin Kwamishinan ‘yan Sanda DCP Abubakar Zubairu ya bada umarnin bincikar lamarin.

Latest stories