Saurari premier Radio
39.9 C
Kano
Wednesday, April 10, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiASUU ta kara tsawaita yajin aiki da makonni 4

ASUU ta kara tsawaita yajin aiki da makonni 4

Date:

Kungiyar malaman Jami’a ta bayyana matakin tsawaita yajin aikin da take yi da mako hudu.

Kungiyar dai ta shafe sama da wata biyar tana yajin aiki bayan gaza cimma matsaya da gwamnatin tarayya, yanzu kuma gashi ta kara wata daya.

Idan har aka shafe wasu mako hudu ba a sasanta tsakanin gwamnati da kungiyar ASUU ba, hakan na nufin ɗaliban Jami’a sun shafe rabin shekara suna zaman jiran tsammani a gida.

Sanarwar da ASUU ta fitar na dauke da sa hannun shugaban kungiyar, Emmanuel Osodeke, an kuma fitar da ita ne bayan kammala wani zaman gaggaawa na jiga-jigan kungiyar jiya Lahadi a Abuja.

ASUU ta godewa ƙungiyar Kwadago ta NLC, da sauran kungiyoyin da suka mara mata baya a zanga-zangar nuna goyon baya da nufin kawo karshen yajin aikin.

Kungiyar ta kara da cewa, ta tsawaita yajin aikin ne da mako hudu, saboda ganin har yanzu gwamnatin tarayya ba ta nuna alamar kawo karshen zaman dalibai a gida ba.

Idan za a iya tunawa, a ranar 14 ga watan Fabrairu ne ASUU ta tsunduma yajin aiki, bisa zargin gwamnatin tarayya da gaza cika alkawuran da ta dauka a yarjejeniyar da suka ƙulla, ciki har da batun inganta rayuwar malamai da dambarwar shigar da kungiyar tsarin biyan albashi na IPPIS da gwamnatin ta fito da shi.

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories