Saurari premier Radio
31.9 C
Kano
Wednesday, April 10, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiAddiniSunusi Lamido ya koka kan lalacewar zamantakewar aure a kasar Hausa

Sunusi Lamido ya koka kan lalacewar zamantakewar aure a kasar Hausa

Date:

Sarkin Kano na 14, kuma Khalifan Darikar Tijjaniyya na Najeria Muhammad Sanusi II ya bayyana wahala da dawainiyar da iyayen amarya ke sha yayin bikin aure a matsayin mafarin matsalalolin zamantakewar aure a kasar Hausa.

Ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa ta Internet, mai taken “Aure a kasar Hausa: Azabar kashe kudi da iyayen yarinya ke sha”

Yayin tattaunawar wadda zauren musulmin London suka shirya, Khalifa Muhammad Sanusi ya kalli aure a kasar Hausa a matsayin araha ga namiji da kuma tsada ga mace, wanda yake ganin ba haka ya kamata lamarin ya kasance ba matukar ana son kawo gyara a zamantakewar aure.

Yace abinda mutane suka fi maida hankali a yanzu shine, maganar rage kayan lefe ba tare an kalli wahalhalun bangaren matan da iyayensu.

Muhammad Sanusi wanda ya kasance bako na musamman, na da ra’ayin cewa saukin da maza ke samu ya sa basa ganin darajar aure, har suke yin saki duk sanda suka ga dama.

A cewar sa, kamata ya yi a juya kudin sadakin zuwa wanda za’a dinga siyan daki da shi, domin da yawan iyaye suna kasa aurar da ‘ya’yan su saboda rashin kudin kayan daki.

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories