Rundunar ‘yan sandan Legas ta sanar da cewa tana cikin shirin ko-ta-kwana bisa zargin ‘yan ta’adda za su kai hare-hare a wasu muhimman wurare a cikin jihar.
Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan jihar, Benjamin Hundeyin ne ya bayyana hakan, a wata sanarwa da ya fitar, inda ya nuna cewa suna sane da yiwuwar fuskantar wasu hare haren ta’addanci a jihar ta legas.
Sanarwar ta kara da cewa, saboda haka jami’an tsaro sun yi shiri na musamman domin maganin duk wani ko wasu da za su iya tada hankulan al’ummar jihar.
A ‘yan kwanakin nan an samu karuwar kai hare-haren ta’addanci a sasan kasar nan ciki har da babban birnin tarayya Abuja.
