24.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabaraiGwamnatin Katsina ta dawo da haramcin hana hawa bubara a jihar

Gwamnatin Katsina ta dawo da haramcin hana hawa bubara a jihar

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Rundunar ‘yan sandan Katsina ta tabbatar da dawo da haramcin hana hawa babura a fadin jihar.

Wannan na zuwa watanni 4 bayan da gwamnatin jihar ta dage haramcin wucin gadi da ta sanyawa masu hawa babur, domin sauƙaƙawa al’umma gudanar da ibadar Azumin watan Ramadana.

Sanarwar da jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda, SP Gambo Isah ya fitar, ta ce saka dokar ta zama dole saboda ganin yadda a baya-bayan nan ‘yan ta’adda ke amfani da babura wajen kai hare-hare.

Katsina na daga cikin jihohin arewa maso yammacin kasar nan dake fama da hare-haren ‘yan bindiga, al’amarin da ya hada da jihohin dake makwabtaka da Katsina wanda suka hada da Kaduna da Zamfara.

Latest stories