Saurari premier Radio
25.9 C
Kano
Saturday, June 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin tarayya za ta siyawa NDLEA motocin kama masu shan kwaya

Gwamnatin tarayya za ta siyawa NDLEA motocin kama masu shan kwaya

Date:

Gwamnatin tarayya ta amince da fitar da Milayan N800, domin sayen motocin aiki guda 32 ga hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, domin inganta ayyukan hukumar.

Da yake ganawa da ‘yan jarida bayan kamala zaman majalisar zartarwa na wannan mako, Ministan yada labarai Alhaji Lai Muhammad ya ce ganin ci gaban da hukumar ke samu wajen yaki da miyagun kwayoyi ya sanya aka amince da fitar da kudin.

A cewar Ministan hakan zai taimakawa hukumar wajen ci gaba da gudanar da aiki tukuru.

Ya kara da cewa kamfanin motoci da ake da shi a nan Najeriya Innoson shi aka bawa kwangilar siyan motocin.

Latest stories

Related stories