Saurari premier Radio
36 C
Kano
Tuesday, June 25, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin tarayya za ta karasa aikin titin Kano zuwa Katsina

Gwamnatin tarayya za ta karasa aikin titin Kano zuwa Katsina

Date:

Majalisar zartarwa ta kasa ta amince da fitar da karin naira miliyan dubu 16 domin karasa aikin fadada babbar hanyar Kano zuwa Katsina

Ministan yada labarai Alhaji Lai Muhammad ne ya bayyana hakan, yayin ganawa da manema labarai ranar alhamis.

Amicewar ta biyo bayan gabatar da kundin aikin fadada titin na Kano zuwa Katsina, mai nisan kilomita 78, wadda aka fara aikinta tun a shekarar 2019.

Bayan da dan kwangilar dake yin aikin ya gabatar da wani bangare na aikin ga gwamnati, kuma gwamnati ta gamsu da aikin ne yasa ta ta kara masa kudi domin ci gaba da aikin.

Haka kuma, ya nemi gwamnati ta duba tsadar kayan ayyuka a yanzu ta kara kudi domin gaggauta karasa aikin.

A don haka ne gwamnatin ta kara naira biliyan 16, inda jumlar kudin aikin ya kasance naira biliyan 46, maimakon biliyan 29 da aka ware tunda fari.

Latest stories

Related stories