24.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabaraiBuhari bai san ’yan bindiga sunyi barazanar sace shi ba – El-Rufai

Buhari bai san ’yan bindiga sunyi barazanar sace shi ba – El-Rufai

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Ahmad Hamisu Gwale

Gwamnan Kaduna Nasir Ahmad El-Rufai ya ce shugaba Buhari ba shi da masaniyar barazanar  da’yan bindiga suka yi na sace shi.

El-Rufa’in ya ce shekara biyar ke nan yana jawo hankalin hukumomin kasar nan kan bin ’yan ta’adda har maboyarsu, amma gwamnatin ta yi watsi da lamarin.

Yace bai kamata ace kasa kamar Najeriya mai tarin jama’a da yawan jami’an tsaro ta gaza kawo karshen ayyukan bata gari ba.

“Idan gwamnatocin da suka shude sun dauki abin wasa don suna ganin yana faruwa ne a iya Zamfara da Katsina da Kaduna da Neja, to yanzu ya zo har inda muke,’’ a cewar El-Rufai.

Sai dai gwamnan yace Shugaba Buhari ya tabbatar masa da cewa yayi zaman tattaunawa na musamman da masu ruwa da tsaki cikin kwanaki hudu da suka gabata.

Latest stories