Saurari premier Radio
26.9 C
Kano
Friday, February 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiAkwai bukatar ayi dokar hana ‘yan siyasa kai 'ya'yansu waje karatu-ASUU

Akwai bukatar ayi dokar hana ‘yan siyasa kai ‘ya’yansu waje karatu-ASUU

Date:

Ahmad Hamisu Gwale

Kungiyar malaman jami’o’i ta kasa ASUU, ta bukaci da’a yi dokar da za ta hana yan siyasa tura ‘ya’yansu kasashen waje yin karatu.

Shugaban kungiyar Malaman jami’oin reshen Jam’iyyar Neja Delta l Farfesa Kingdom Tombra ne ya bayyana hakan.

Farfesa Tombra ya ce yin dokar zai bai wa jami’o’in kasar nan damar su samu ci gaba da kuma samun ingantattun kayan aiki.

Ya kara da cewa, ba wai kungiyoyin na yin zanga-zangar ba ne don muzgunawa al’umma, sai don ci gaban kasar nan da kuma bunkasar ilimi.

Ya ce yin makaranta daya tsakanin ‘ya’yan talakawa da na mahukuntan zai taimaka wajen magance matsalolin da ilimi ke fuskanta.

Tsahon watanni shida ke nan malaman jami’o’in kasar nan suna yajin aiki.

Wanann ne kuma ya janyo kungiyar kwadago NLC ta gudanar da zanga-zangar kwanaki 2 a fadin kasa, domin nuna goyon baya ga malaman kan bukatunsu ga gwamnati.

 

Latest stories

Related stories