Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Saturday, June 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiWaiwaye kan shari'ar kisan Hanifa Abubakar

Waiwaye kan shari’ar kisan Hanifa Abubakar

Date:

Muhammad Bello Dabai

Wata babbar kotun tarayya dake jihar Kano, ta yanke hukuncin kisa ga Abdulmalik Tanko, wanda aka tuhuma da sacewa tare da hallaka Hanifa Abubakar, yar shekaru 5.

Wannan ya biyo bayan kamashi da laifukan, bayan tsawon  lokaci ana gudanar da shari’a, tare da gabatar da shaidu.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Usman Na’Abba ne ya yanke hukuncin, bayan karanto laifukan da ake zargin Abdulmalik da aikatawa.

Tushen labarin

Tun dai a ranar 4 ga watan Disambar shekarar 2021 ne labarin sace Hanifa ya karade shafukan sada zumunta, inda wasu matasa a Adaidai sahu suka yaudareta akan zasu dana ta, tare da yan uwanta dalibai, yayin dawowarsu daga makaranta a yammacin ranar.

Lamarin ya faru ne a unguwar Kawaji dake karamar hukumar Nasarawa a jihar Kano.

Daga nan ne kuma, ba’a sake jin duriyar yarinyar ba, duk da zurfafa bincike da jami’an tsaro suka yi, baya ga yada hotunanta a shafukan sada zumunta.

A wannan lokaci, anyi kokwanton cewa masu garkuwa da mutane ne suka dauke ta, ko kuma barayi, kasancewar ba’a fiye samun irin matsalar a jihar Kano ba.

To sai dai, daga baya, barayin yarinyar sun tuntubi iyayenta, ba tare da sanar dasu ainahin manufarsu ta dauke yarinyar ba.

Labarin sace Hanifa, yayi matukar tada hankalin al’umar unguwar Kawaji, inda mazauna yankin suka shiga dari darin aika yayansu makaranta.

Yadda Aka Gano Gawar ta

Sakamakon yadda hadin gwiwar jami’an tsaro na yan sanda da DSS suka zurfafa bincike, biyo bayan tuntubar iyayen Hanifa da barayin sukayi, inda suka nemi a biyasu naira miliyan 6 a matsayin kudin fansa, lamarin ya kai ga kama Abdulmalik Tanko, da wani abokinsa mai sun Hashimu.

Kamar yadda kawun Hanifa Suraj Zubair ya labartawa Premier Radio, an shirya dabarun kama barayin ne ta hanyar amincewa da biyansu kudin fansar, har suka sanya wurin da suke son a ajiye kudin.

Bayan ajiye kudin fansar a inda suka (Barayin) bukata ne, jami’ai suka cigaba da sanya ido, domin gano masu daukar.

“Kwatsam sai aka hangi Abdulmalik Tanko na zarya a wurin, sai jami’an suka tuhumeshi kan me yazo yi, amma ya rasa abin fada, a nan ne ya shiga hannu” Inji Suraj Zubair.

Sakamakon binciken jami’an dai ya kai ga tonuwar asirin Abdulmalik, inda ya fara labarta musu yadda lamarin ya faru.

Ya tabbatar musu da cewa shi malamin Hanifa ne, dake koyar da ita a makarantar Noble Kids Academy, kuma bayan ya dauke ta, tare da taimakon abokinsa Hashim, da kuma wata mata Fatima Jibril musa, ya kaita gidansa.

Abdulmalik ya shaidawa jami’an cewa bayan ya fahimci ana bibiyarsa, a ranar 18 ga watan Disambar 2021 ya sanyawa yarinyar maganin Bera a abinci, taci ta mutu.

Domin gudun tonuwar asirinsa, ya hada baki da abokan laifin nasa, inda suka sanya ta a buhu tare da binne ta a makarantar Prestige Academy dake unguwar Tudun Murtala Kwanar Yan Ghana.

Yadda Al’ummar Kano Sukayi Alhinin kisanta

Labarin gano gawar Hanifa cikin yana mai matukar razani, na zuwa ne sama da kwanaki 40 da sace ta.

Wannan ne batun da ya karade shafukan sada zumunta, tare da zama babban maudu’in tattaunawa a kafafen yada labarai, inda al’umma sukayi ta bayyana alhini da kuma hukuncin da suke fatan ganin an yankewa barayin.

Babban abinda yafi daga hankalin al’ummar Kano shine, yadda aka gano hannun malamin Hanifa a sace ta, wato Abdulmalik Tanko.

Wannan tasa al’umma daga sassa daban daban na Najeriya, da suka hadar da yan siyasa, yan kasuwa da malamai zuwa ta’aziyyar yarinyar ga iyayenta.

Daga cikin masu ta’aziyyar, har da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, sai ministan sadarwa Farfesa Isah Ali Fantami, da mai dakin shugaban kasa Aisha Buhari, sai gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, da manyan mukarraban gwamnatinsa.

Kiraye Kirayen ‘Yan Fafutuka

Batun sace Hanifa, yayi matukar jan hankalin kungiyoyi da daidaikun yan fafutukar kare hakkin dan adam a nan Kano dama kasa baki daya.

Galibi a wannan lokacin, sun matsawa gwamnati lamba kan amincewa dokar kare yancin mata da kananan yara.

A cewar wani dan fafutuka, daga kungiyar Human Rights Watch, Malam Karibu, amincewa dokar zai taimaka wajen dakile faruwar irin wadannan munanan laifuka.

To sai dai a wata ziyara da shugaban majalisar dokokin jihar Kano Hamisu Ibrahim Chidari ya kawo Premier Radio, ya shaida cewa, tuntuni majalisar na cigaba da nazartar dokar, domin tayi daidai da tsarin addini da al’adar mutanen Kano.

Yace suna tattaunawa da malaman addini da jagororin gargajiya wajen tabbatar da ita, kuma da zarar sun kammala, zata shiga jerin dokokin jihar Kano.

Ina Aka Dosa?

Yanzu haka dai, kotu ta yankewa Abdulmalik Tanko hukuncin kisa ta hanyar rataya, bisa laifin garkuwa da kuma kashe Hanifa, sannan da daurin shekaru 5 a gidan yari, na laifin garkuwa da mutum.

Har ila yau, kotun ta kuma yankewa Fatima Musa, abokiyar laifin Abdulmalik hukuncin daurin shekaru 2, a matsayinta na uwa, kuma wadda aka samu da hannu a cikin wannan manakisa.

Shima abokin Abdulmalik, wato Hashim, an yanke masa hukuncin daurin shekaru 2 a gidan kaso, sannan daga baya a kashe shi.

To amma, kamar yadda tsarin doka yayi tanadi, Abdulmalik da sauran abokan laifinsa nada damar daukaka kara zuwa kotun gaba, idan basu gamsu da hukuncin babbar kotun tarayyar dake Kano ba, har zuwa matakin kotun koli, wato Supreme Court.

Rashin mika shari’ar gaba na nufin dukkaninsu, sun amince da hukuncin da aka yanke musu.

Latest stories

Related stories