Saurari premier Radio
21.8 C
Kano
Saturday, March 2, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin KanoKYAN ALKAWARI: Shin Ganduje zai sanya hannu a kashe Abdulmalik?

KYAN ALKAWARI: Shin Ganduje zai sanya hannu a kashe Abdulmalik?

Date:

Mukhtar Yahya Usman

Watanni shida ke nan da gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya yi alkawarin sanya hannun don kashe Abdulmalik Tanko wanda ya kashe Hanifa da zarar kotu ta yanke masa hukuncin kisa.

Gwaman ya yi wannan furuci ne a ranar wata Litinin 25 ga Janairun wannan shekara lokaci  da ya kai ta’aziyya gidan su Hanifan bayan kasheta.

Abdulmalik Tanko yad ai yi garkuwa da yarinyar ne a watan Disamba kuma suka nemi kudin fansaNaira miliyan 6.

Duk da haka, a cikin watan Janairu, Abdulmalik  ya kashe Hanifa da “maganin bera”, kuma ya binne gawarta a harabar makarantarrsa tare da taimakon wani abokinsa.

Da yake jawabi yayin ziyarar, gwamnan ya tabbatar wa ‘yan uwa cewa za a yi adalci a shari’ar, ya kuma kara da cewa za a gaggauta shari’a.

Sai dai abin zuwabawa idanu a nan shi ne ko gwamnan zai cika wancan alkawari da ya dauka na sanya hannu kan kisan? Wannan shi ne abinda idan nuna jama’a ya kai kai.

Ko da yake wasu na ganin gwamnan ya yi wadancan kalamai ne don kwantar da hankalin iyayen yarinyar da aka kashe, ya yin da was uke ganin gwamnan zai aikata.

A yanzu dai tuni kotu ta yankewa Abdulmali da Hashim hukuncin kisa ta hanyar Rataya, abin jira a gani shi ne matakin da gwaman zai dauka.

Latest stories

CBN Ya Kwace Lasisin Yan Canji Sama da Dubu Hudu A Faɗin Nijeriya

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanar da soke lasisin...

Dangote ya bayar da shawarar mayar da kasuwar waya ta Farm Center zuwa cibiyar fasaha

Fitaccen attajirin nan, Alhaji Aliko Dangote, ya shawarci jami'ar...

Related stories

CBN Ya Kwace Lasisin Yan Canji Sama da Dubu Hudu A Faɗin Nijeriya

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanar da soke lasisin...

Dangote ya bayar da shawarar mayar da kasuwar waya ta Farm Center zuwa cibiyar fasaha

Fitaccen attajirin nan, Alhaji Aliko Dangote, ya shawarci jami'ar...