Saurari premier Radio
21.8 C
Kano
Saturday, March 2, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiBa mu fara karbar kudin aikin hajjin bana ba inji hukumar alhazai

Ba mu fara karbar kudin aikin hajjin bana ba inji hukumar alhazai

Date:

Mukhtar Yahya Usman
Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano ta ce har yanzu bata fara karbar kudin ajiya na aikin hajjin bana ba.

Haka kuma hukumar ta ja hankalin jama’a da kada su sanya kudadensu a hannun wani banki ko wasu mutane da sunan fara biyan kudin aikin hajjin na bana.

Shugaban hukumar Alhaji Muhammad Abba Danbatta ne ya bayyana hakan ya yin da yake zantawa da manema labara kan fara shirye-shiryen aikin Hajjin bana.

Ya ce hukumar bata kira mutane ko kuma bude wata cibiya da za a karbi kudin maniyyata a bana ba.

Muhammad Danbatta ya ce duk da cewa har yanzu suna jiran hukumar NAHCON ta sanar da su adadin maniyyatan da za a baiwa Kano, za su baiwa wadanda suka bar kudadensu ne fifiko.

“Idan NAHCON ta bamu dama za mu fara la’akari da wadanda suka bar kudaden su ne a bara da bara waccan lokacin da KORONA ta hana jama’a zuwa aikin Hajji.

“A yanzu ba zamu karbi kudin kowa ba har sai wadancan sun samu shiga ko kuma sun ce sun janye da kansu” Ya ce.

Ya ce a yanzu haka hukumar ta mayarwa da maniyyata sama da N Milyan 440 ga miniyyatan da suka ajiye kudadensu a bara da bara waccen da suka bukaci a dawo musu da kudadensu

Latest stories

CBN Ya Kwace Lasisin Yan Canji Sama da Dubu Hudu A Faɗin Nijeriya

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanar da soke lasisin...

Dangote ya bayar da shawarar mayar da kasuwar waya ta Farm Center zuwa cibiyar fasaha

Fitaccen attajirin nan, Alhaji Aliko Dangote, ya shawarci jami'ar...

Related stories

CBN Ya Kwace Lasisin Yan Canji Sama da Dubu Hudu A Faɗin Nijeriya

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanar da soke lasisin...

Dangote ya bayar da shawarar mayar da kasuwar waya ta Farm Center zuwa cibiyar fasaha

Fitaccen attajirin nan, Alhaji Aliko Dangote, ya shawarci jami'ar...