Saurari premier Radio
26.4 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiSukar Ganduje: Kotu ta aike da Danbilki Kwamada kurkuku

Sukar Ganduje: Kotu ta aike da Danbilki Kwamada kurkuku

Date:

Alkalin kotun Mai Shari’a Aminu Gabari ne ya ba da umarnin yayin zaman kotun a ranar Talata.

Hakan ya biyo bayan yin watsi da bukatar lauyoyin Danbilki Kwamanda kan ba da belinsa.

An dai gurfanar da Kwamanda ne bisa laifuka uku, da suka kunshi bata sunan Ganduje.

Ciki harda zargin gwamnan da bayar da cin hanci ga shugabancin riko na APC Mai Mala Buni, don tsaginsa ya karbi takardar zama halastaccen shugabancin jam’iyyar a Jihar Kano.

Alkalin dai ya aike da shi gidan kason ne bayan ya ki amincewa da bukatar lauyoyinsa kan bayar da shi beli.

Sai dai wanda ake zargin ya musanta aikata laifukan da ake zarginsa da su.

Daga nan ne alkalin ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa 15 ga watan Maris din 2022, tare da umarnin ci gaba da tsare shi a kurkuku har zuwa lokacin.

Danbilki Kwamanda dai tsawon lokaci ya yi kaurin suna wajen sukar Ganduje a akasarin shirye-shiryensa a gidajen rediyon da ke ciki da wajen Jihar.

Sai dai ba shi ne mai sukar Gwamnan na farko da aka taba tsarewa a kurkuku ba.

Idan za a iya tunawa, ko a watan Janairun 2022 da ya gabata, sai da aka tsare tsohon Kwamishina a gwamnatin Gandujen, Injiniya Mu’azu Magaji saboda zargin aikata makamancin wannan laifin, har sai da ya cika sharudan belin nasa.

Latest stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

Related stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...