Saurari premier Radio
25.1 C
Kano
Saturday, July 27, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiHukumar ICPC ta gurfanar da shugaban karamar hukumar Fagge a gaban kotu

Hukumar ICPC ta gurfanar da shugaban karamar hukumar Fagge a gaban kotu

Date:

Mukhtar Yahya Usman

Kotu a Kano ta fara sauraron karar da hukumar ICPC ta shigar da shugaban karamar hukumar Fagge Ibrahim Muhammad Shehi bisa zargin almundahana.

A cewar hukumar, tana zargin shugaban karamar hukumar da hada baki da da wasu ma’aikatan hukumar tara kudaden haraji wajen aikata almundahana da badakalar kudade.

Ta ce yana baiwa wasu daga cikin ma’aikatan tara kudaden hariji kaso 20 na kudaden da ake tarawa a matsayin kasansu, wanda hakan ya saba ka’ida.

Hukumar ta ce kaso 2 zuwa 5 ne kason da ya kamata a baiwa ma’aikatan amma ake basu 20 da nufin ya kewaye ya karbi rabonsa.

Sai dai shugaban karamar hukumar ya musata zargin.

A zaman kotun na ranar Litinin hukumar ta gabatar da shaida na farko, inda kuma ta yi alkawarin gabatar da ragowar shaidun a nan gaba.

Haka kuma alkalin kotun Jamilu Shehu sulaiman ya dage sauraron karar har zuwa ranar 15 ga watan Mayun wannan shekara domin ci gaba da sauraron karar.

Latest stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

Related stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...