Saurari premier Radio
40.5 C
Kano
Sunday, May 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiAn rantsar da Abdullahi Abbas a matsayin shugaban APC na Kano

An rantsar da Abdullahi Abbas a matsayin shugaban APC na Kano

Date:

Muhammad Bello Dabai

Kwamatin rikon APC na kasa, karkashin sabon shugabansa, gwamnan jihar Neja Abubakar Sani Bello, ya rantsar da Abdullahi Abbas a matsayin sabon shugaban jam’iyyar na jihar Kano.

Wannan na zuwa ne jim kadan bayan shigar Bello Ofishi, tare da yin waje da Buni.

A baya dai uwar jam’iyyar ta gabatar da shaidar shugabanci ga Abdullahi Abbas, bayan da kotun daukaka kara tayi watsi da hukuncin wata kotun tarayya dake Abuja, wadda ta halasta shugabancin tsagin G7 karkashin Alhaji Ahmadu Haruna Zago.

Tuni dai tsagin na G7 ya daukaka kara zuwa kotun koli, inda yayi zargin yi masa rashin adalci.

Ar ila yau zaman sulhun da akayi, ya gaza shawo kan rikicin, inda bangaren Sanata ya bada sharadin sai an bashi mukamai sama da kaso 50% kafin su amince.

Billar G7 a jihar Kano

Tun dai a watannin baya, wasu hotuna suka billa shafukan sada zumunta, waɗanda ke nuna Sanata Ibrahim Shekarau, da Sanatan Kano ta arewa Barau Jibrin, da kuma Sanatan Kano ta Kudu, Kabiru Gaya, sai dan majalisar wakilan tarayya dake wakiltar karamar hukumar Birni, Sha’aban Sharada, da dai sauransu, a babban birnin tarayya Abuja.

Rahotannin da suka biyo baya, suka tabbatar cewa wannan tawagar, tayi tattaki na musamman ne zuwa uwar jam’iyyar APC ta kasa domin gabatar da koke kan mayar da su saniyar ware a jihar Kano.

Jim kadan bayan taron, aka fidda wata sanarwa dauke da sa hannun jiga jigan tafiyar su 7, wanda daga nan ne sunan tsagin na G7 ya billa.

To sai dai, cikin takardar sanya hannun, ba’a ga na Sanata Kabiru Gaya ba, wanda daga baya, ya barranta kansa da tafiyar, yana mai cewa ba zai ci amanar gwamna ba.

Zaben shugabannin jihohi

A jihar Kano, jam’iyyar APC ta gudanar da zaben shugabanni ne guda biyu, da suka hadar da na tsagin G7 karkashin jagorancin tsojon gwamna Ibrahim Shekarau, da kuma bangaren gwamna Ganduje.

Zaben na 16 ga Oktobar shekarar 2021, ya fidda Abdullahi Abbas a matsayin shugaban da yayi nasara a bangaren gwamna, sai Ahamdu Zago, wanda tsagin Shekarau na G7 ya zaɓa.

Wannan ce ta kai ga gudunar da shubancin jam’iyyar guda biyu na tsawon lokaci, kafin hukuncin kotun daukaka kara, wanda ya halasta tsagin gwamna.

Kafin hakan kuma, uwar jam’iyyar ta APC ta aiko da kwamatin sulhunta bangarorin biyu, wanda ya nuna goyon baya karara ga tsagin gwanma.

Wannan tasa bangaren G7 sukayi watsi da kwamatin.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...