Saurari premier Radio
39.9 C
Kano
Thursday, April 18, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiYanzu-Yanzu: Gwamnan Neja ya zama shugaban riko APC

Yanzu-Yanzu: Gwamnan Neja ya zama shugaban riko APC

Date:

Muhammad Bello Dabai

Gwamnan  jihar Neja Abubakar Sani Bello, ya maye gurbin Shugaban kwamatin rikon jam’iyyar APC na kasa, gwamnan Yobe, Alhaji Mai Mala Buni.

Wannan na zuwa ne jim kaɗan bayan isowar Bello sakatariyar jam’iyyar ta kasa dake Abuja, bisa rakiyar jami’an tsaro.

Rahotanni sun bayyana cewa an samu yar hayaniya bayan da Buni yayi gaddamar fita daga ofishin.

To sai da bisa taimakon jami’an tsaro, an raka Abubakar Bello zuwa ofishin.

Jim kaɗan bayan zamansa a kujera, aka gabatar masa da shugabannin jam’iyyar na jihohi da aka zaɓa domin rantsarwa, cikinsu har da na jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas.

Da safiyar yau Litinin dai, sakataren jam’iyyar  na kasa Mr. John James Akpanudoedehe, a wata sanarawa ya musanta labarin dake cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kori Buni.

Ana dai alakanta matakin da batun babban taron jam’iyyar na kasa, inda za a zaɓi sabbin shugabannin da za su kai jam’iyyar ga zaben 2023.

A karshen makon nan ne dai shugabannin jam’iyyar na jihohi suka raba gari da gwamnonin APC kan wanda za’a marawa baya ya shugabanci jam’iyyar.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna goyon bayansa karara ga stohon gwamnan jihar Nassarawa, Sen. Adamu Abdullahi, da tsohon shugaban majalisar dattawa Sen. Ken Nnamani.

To sai dai gwamnoni na ganin wannan zaɓi a matsayin barazana, bisa abinda suka kira damƙawa riƙakkun yan PDP jam’iyyar.

Latest stories

Dan Ganduje ya kai wa Muhuyi ziyarar goyan bayan a binciki mahaifansa

Dan tsohon gwamnan Kano, Abdulaziz Abdullahi Ganduje, ya kai...

Farashin Dizel ya koma 1000 a Najeriya

Rahotanni sun bayyana matatar mai ta Dangote ta sanar...

Related stories

Dan Ganduje ya kai wa Muhuyi ziyarar goyan bayan a binciki mahaifansa

Dan tsohon gwamnan Kano, Abdulaziz Abdullahi Ganduje, ya kai...

Farashin Dizel ya koma 1000 a Najeriya

Rahotanni sun bayyana matatar mai ta Dangote ta sanar...