Saurari premier Radio
24.8 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabarai'Yan PDP da dama sun fita daga jam'iyyar a karamar hukumar Rano

‘Yan PDP da dama sun fita daga jam’iyyar a karamar hukumar Rano

Date:

Mukhtar Yahya Usman

Wasu ‘yan kungiar Kwankwaso ‘kafarka kafarmu’ a karamar hukumar Rano sun ajiye mukamansu a jam’iyyar PDP bisa zarigin yi musu ba daidai ba.

Mutanen da suka hadar da shugabannin mazabu 10 da ke karamar hukumar sunce sun bar jam’iyyar PDP ne saboda rashin adalcin da ake nuna musu.

Haka kuma sun ce sun yanke shawarar bin tsohon gwamann Kano Rabi’u Musa Kwankwaso duk inda zai koma da zarar ya fice daga jam’iyyar.

A zantawarsa da PREMIER RADIO shugaban kungiyar Yusuf Bala ya ce tuni suka aike da takardarsu zuwa ga ofishin jam’iyya na karamar hukumar ta Rano kan matakin da suka dauka.

Ya ce sun yanke shawarar hakan ne la’akari da yadda ake mayar da su saniyar ware kuma ake nuna fifiko kan yadda ake tafiyar da al’amuran jam’iyyar a karamar hukumar.

“Mun fice daga jam’iyyar PDP ne saboda rashin bin tsarin dimokuradiyya a jam’iyyar tun daga shiyya zuwa matakin kasa, musamman yankin mu na Arewa.

“Za mu bi sahun Kwankwaso zuwa kowace jam’iyyar siyasar da zai je saboda mun amince da shi da kuma akidarsa ta siyasa.”

Sai dai da take mayarda martani jam’iyyar PDP a jihar Kano ta ce bata da masaniya kan wannan al’amari.

Jami’in yada labaran jam’iyyar a nan Kano Bashir Santa ya ce shima dai yaga batun ne a shafukan sada zuminta.

Ya ce irin haka na faruwa a siyasa, wasu suga ba a yi musu adalci ba, su kuma nemi hakkinsu.

Amma dai ya tabbatar da cewa har yanzu ba a aike musu da takardar ficewar ta su ba daga karamar hukuma, kamar yadda suka yi ikirarin sun aika a rubuce.

Latest stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

Related stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...