Saurari premier Radio
41.9 C
Kano
Friday, April 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiYadda DSS ta gayyaci shugabannin kanan hukumomi uku a Kano

Yadda DSS ta gayyaci shugabannin kanan hukumomi uku a Kano

Date:

Mukhtar Yahya Usman
Shugaban karamar hukumar Birni Fa’izu Alfindiki ya ce shi da wasu jami’an gwamnatin Ganduje sun mika kansu ne ga hukumar tsaro ta DSS bayan da ta gayyace su ba wai kamasu ta yi ba.

Alfindiki ya bayyana hakan ne ya yin da yake zantawa da sashin Hausa na BBC ranar Laraba.

Hukumar DSS ta gayyaci Fa’izu ne da wasu na gaba-gaba a tsagin gwamna Ganduje domin amsa tambayoyi bisa zargin aikata daba.

Sauran mutanen sun hada da Khalid Ishaq Diso, shugaban karamar hukumar Gwale; da Injiniya Bashir Kutama, shugaban karamar hukumar Gwarzo.

Ya ce an gayyaci mutumin da ke son jam’iyyar APC ta tsayar da shi takarar gwamnan jihar ta Kano a zaben 2023, A.A Zaura; da shugaban hukumar KAROTA, Baffa Babba Dan Agundi, da kuma wani mai bai wa Gwamna shawara.

An rantsar da Abdullahi Abbas a matsayin shugaban APC na Kano

Matasa biyar sun mutu yayin hakar kasa a Kano

Sukar Ganduje: Kotu ta aike da Danbilki Kwamada kurkuku

Rahotanni sun nuna cewa ana zargin wasu daga cikinsu da hannu a manyan-manyan hare-haren daba, lamuran da suka yi sanadin mutuwar wasu mutane.

Ko da a makon jiya, rahotanni sun tabbatar da cewa magoya bayan Murtala Sule Garo da na dan majalisar wakilai Kabiru Alasan Rurum sun yi arangama a karamar hukumar Rano lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama

A baya bayan nan dai ‘yan siyasa musamman na jam’iyyar APC sun rika sukar juna bayan raba gari tsakanin bangaren Gwamna Ganduje da tsohon Gwamna Ibrahim Shekarau, sai dai tun kafin hakan an rika jifan juna da muggan kalamai da kuma amfani da ‘yan daba domin biyan bukatu na siyasa.

Hakan kuwa ya yi kamari ne bayan da mai dakin gwamnan jihar Kano, Hafsatu Ganduje, ta yi nuni da cewa Kwamishinan kananan hukumomi, Murtala Sule Garo ne ya dace ya gaji mjinta a zaben gwamna na 2023.

‘Yan siyasa da dama sun fassara kalaman da cewa alama ce ta cewa tuni aka ware ‘yan bora da ‘yan mowa kuma an rufe kofa ga duk wanda yake neman zama gwamnan jihar ta Kano a karkashin jam’iyyar APC. To amma

daga bisani gwamnatin jihar ta bayyana cewa ba a fahimci kalaman mai dakin gwamnan ba ne.

Tun daga wancan lokaci ne yanayin siyasa ya kara yin zafi tsakanin bangaren Murtala Sule Garo da kuma Sanata Barau Jibrin, wanda shi ma ake rade-radin yana son tsayawa takarar gwamnan jihar Kano a zaben 2023.

Kazalika hukuncin da wata kotun daukaka kara ta yanke inda ta bai wa bangaren Ganduje nasara a shugabancin jam’iyyar APC a Kano ya ta’azzara yanayin siyasar da ake ciki a jihar.

Masana harkokin siyasa irin su Farfesa Kamilu Sani Fagge sun ce kokawar neman iko na cikin abubuwan da suka ta’azzara amfani da ‘yan daba wajen cimma buri na siyasa.

Latest stories

NPFL: Gwamnatin Kano ta bawa Kano Pillars wasa Uku domin ta yi Nasara

Gwamnatin Jihar Kano ta bawa kungiyar Kwallon kafa ta...

Dan Ganduje ya kai wa Muhuyi ziyarar goyan bayan a binciki mahaifansa

Dan tsohon gwamnan Kano, Abdulaziz Abdullahi Ganduje, ya kai...

Related stories

Dan Ganduje ya kai wa Muhuyi ziyarar goyan bayan a binciki mahaifansa

Dan tsohon gwamnan Kano, Abdulaziz Abdullahi Ganduje, ya kai...

Farashin Dizel ya koma 1000 a Najeriya

Rahotanni sun bayyana matatar mai ta Dangote ta sanar...